Littafi Mai Tsarki

Zab 116:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,Allahnmu mai rahama ne.

6. Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.

7. Kada ki yi shakka, ya zuciyata,Gama Ubangiji yana yi mini alheri.

8. Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,Ya share hawayena,Bai bari a kāshe ni ba.

9. Don haka nake tafiya a gaban UbangijiA duniyar masu rai.

10. Na dai yi ta gaskatawa, ko da yakeNa ce, “An ragargaza ni sarai.”