Littafi Mai Tsarki

Zab 109:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ka sa waɗanda suke binsa bashi su kwasheDukan abin da yake da shi.Ka sa baƙi su kwashe dukan abin da ya sha wahalar nema.

12. Ka sa kada kowa ya yi masa alheri sam,Kada ka bar kowa ya lura da marayunsa.

13. Ka sa dukan zuriyarsa su mutu,Har a manta da sunansa a tsara mai zuwa.

14. Sai ka tuna, ya Ubangiji, da muguntar kakanninsa,Kada ka manta da zunuban mahaifiyarsa.

15. Ka tuna da zunubansu kullayaumin, ya Ubangiji,Amma su kansu a manta da su ɗungum!

16. Gama mutumin nan bai taɓa tunanin yin alheri ba,Yakan tsananta wa talakawa, da matalauta, da kasassu, har ya kashe su.

17. Yana jin daɗin la'antarwa, ka sa a la'anta shi!Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!

18. Yakan la'antar a sawwaƙe kamar yadda yake sa tufafinsa.Ka sa la'antarwa da yake yiSu jiƙa shi kamar ruwa,Su shiga har ƙasusuwansa kamar mai,