1. Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!
2. Mugaye da maƙaryata sun tasar mini,Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.
3. Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina.Suna tasar mini ba dalili.
4. Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu,Har ina yi musu addu'a.
5. Sukan sāka mini alheri da mugunta,Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.