Littafi Mai Tsarki

Zab 109:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!

2. Mugaye da maƙaryata sun tasar mini,Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.

3. Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina.Suna tasar mini ba dalili.

4. Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu,Har ina yi musu addu'a.