Littafi Mai Tsarki

Zab 109:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!

2. Mugaye da maƙaryata sun tasar mini,Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.

3. Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina.Suna tasar mini ba dalili.

4. Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu,Har ina yi musu addu'a.

5. Sukan sāka mini alheri da mugunta,Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.

6. Ka zaɓi lalataccen mutum ya shara'anta maƙiyina,Ka sa ɗaya daga cikin maƙiyansaYa gabatar da ƙararsa.

7. Ka sa a same shi da laifi a shari'ar da ake yi masa,Ka sa har addu'ar da yake yiTa zama babban laifi!

8. Ka aukar masa da ajalinsa nan da nan,Ka sa wani ya ɗauki matsayinsa!

9. Ka sa 'ya'yansa su zama marayu,Matarsa kuwa ta zama gwauruwa!

10. Ka sa 'ya'yansa su rasa gidan zama, su riƙa yawon bara.Ka sa a kore su daga kufan da suke zaune!

11. Ka sa waɗanda suke binsa bashi su kwasheDukan abin da yake da shi.Ka sa baƙi su kwashe dukan abin da ya sha wahalar nema.

12. Ka sa kada kowa ya yi masa alheri sam,Kada ka bar kowa ya lura da marayunsa.

13. Ka sa dukan zuriyarsa su mutu,Har a manta da sunansa a tsara mai zuwa.