Littafi Mai Tsarki

Zab 108:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?Wa zai kai ni Edom?

11. Da gaske ka yashe mu ke nan?Ba za ka yi tafiyaTare da sojojinmu ba?

12. Ka taimake mu, mu yaƙi abokin gāba,Domin taimako irin na mutum banza ne!

13. Idan Allah yana wajenmu,Za mu yi nasara,Zai kori abokan gābanmu.