1. A shirye nake, ya Allah,Na shirya sosai!Zan raira waƙa in yabe ka!Ka farka, ya raina!
2. Ku farka, ya molona da garayata!Zan farkar da rana!
3. Zan yi maka godiya a tsakiyar sauran al'umma, ya Ubangiji!Zan yabe ka a tsakiyar kabilai!
4. Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai,Amincinka kuma ya kai sararin sammai.