Littafi Mai Tsarki

Zab 107:9-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa,Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.

10. Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa,'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,

11. Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki,Sun kuwa ƙi koyarwarsa.

12. Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki,Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.

13. A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

14. Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa,Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.

15. Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

16. Ya kakkarya ƙofofin da aka yi da tagulla.Ya kuma ragargaza ƙyamaren da aka yi da baƙin ƙarfe.

17. Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu,Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.

18. Ba su so su ga abinci,Sun kusa mutuwa.

19. A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.

20. Da umarninsa ya warkar da su,Ya cece su daga kabari.

21. Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

22. Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu,Su raira waƙoƙin murna,Su faɗi dukan abin da ya yi!