Littafi Mai Tsarki

Zab 107:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce!

2. Ku zo mu yabi Ubangiji tare,Dukanku waɗanda ya fansa,Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.

3. Ya komo da ku daga ƙasashen waje,Daga gabas da yamma, kudu da arewa.

4. Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya,Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.

5. Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa,Suka fid da zuciya ga kome.

6. Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga wahalarsu.