Littafi Mai Tsarki

Zab 107:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce!

2. Ku zo mu yabi Ubangiji tare,Dukanku waɗanda ya fansa,Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.

3. Ya komo da ku daga ƙasashen waje,Daga gabas da yamma, kudu da arewa.