Littafi Mai Tsarki

Zab 106:25-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni,Sun ƙi su saurari Ubangiji.

26. Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi,Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,

27. Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna,Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.

28. Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor,Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.

29. Suka tsokani Ubangiji, ya yi fushi saboda ayyukansu,Mugawar cuta ta auka musu,

30. Amma Finehas ya tashi, ya yanke hukunci a kan laifin,Aka kuwa kawar da annobar.