Littafi Mai Tsarki

Zab 105:20-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sa'an nan Sarkin Masar ya sake shi,Mai mulkin dukan sauran al'umma ya 'yantar da shi.

21. Ya sa shi ya lura da mulkinsa,Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.

22. Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma'aikatan hukuma.Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.

23. Sa'an nan Yakubu ya tafi Masar,Ya zauna a ƙasar.

24. Ubangiji ya sa jama'arsa suka hayayyafa da yawa,Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.

25. Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa,Suka yi wa bayinsa munafunci.

26. Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.

27. Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.

28. Ya aika da duhu a bisa ƙasar.Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.

29. Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,Ya karkashe kifayensu duka.

30. Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.

31. Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwariSuka cika dukan ƙasar.

32. Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsuMaimakon ruwan sama.

33. Ya lalatar da 'ya'yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu,Ya kakkarya itatuwansu.

34. Ya ba da umarni, sai fāri suka zo,Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.

35. Suka cinye dukan tsire-tsire na ƙasa.Suka cinye dukan amfanin gonaki.