Littafi Mai Tsarki

Zab 105:10-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,

11. “Zan ba ka ƙasar Kan'ana,Za ta zama mallakarka.”

12. Jama'ar Ubangiji kima ne,Baƙi ne kuwa a ƙasar.

13. Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,Daga wannan mulki zuwa wancan,

14. Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.

15. Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu,Kada ku cuci annabawana!”

16. Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu,Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,

17. Sai ya aika da Yusufu ya riga su zuwa,Shi wanda aka sayar da shi kamar bawa.

18. Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarƙa,Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe,

19. Har kafin faɗar da ya yi, ta cika.Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.

20. Sa'an nan Sarkin Masar ya sake shi,Mai mulkin dukan sauran al'umma ya 'yantar da shi.

21. Ya sa shi ya lura da mulkinsa,Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.

22. Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma'aikatan hukuma.Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.

23. Sa'an nan Yakubu ya tafi Masar,Ya zauna a ƙasar.

24. Ubangiji ya sa jama'arsa suka hayayyafa da yawa,Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.

25. Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa,Suka yi wa bayinsa munafunci.