Littafi Mai Tsarki

Zab 104:19-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai,Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.

20. Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.

21. Sagarun zakoki sukan yi ruri sa'ad da suke farauta,Suna neman abincin da Allah zai ba su.

22. Sa'ad da rana ta fito,Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.

23. Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,Su yi ta aiki har maraice ya yi.

24. Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa!Da hikima ƙwarai ka halicce su!Duniya cike take da talikanka.

25. Ga babbar teku mai fāɗi,Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune,Manya da ƙanana gaba ɗaya.

26. Jiragen ruwa suna tafiya a kansa,Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.

27. Dukansu a gare ka suke dogara,Don ka ba su abinci sa'ad da suke bukata.

28. Ka ba su, sun ci,Ka tanada musu abinci, sun ƙoshi.