1. Ka yabi Ubangiji, ya raina!Ya Ubangiji Allahna, mai girma ne kai!Kana saye da ɗaukaka da daraja,
2. Ka yi lulluɓi da haske.Ka shimfiɗa sammai kamar alfarwa.
3. Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama.Gajimare ne karusanka,A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.
4. Iska ce jakadanka,Walƙiya kuwa ita ce baiwarka.
5. Ka sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta,Ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.
6. Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba,Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.
7. Amma sa'ad da ka tsauta wa ruwa,Sai ya tsere,Sa'ad da ya ji ka daka tsawa,Sai ya sheƙa a guje.
8. Ya haura kan duwatsu, ya gangara cikin kwaruruka,Wurin da ka shirya masa.