Littafi Mai Tsarki

Zab 103:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma ƙaunar Ubangiji ga waɗanda suke girmama shi har abada ce.Alherinsa kuwa tabbatacce ne har dukan zamanai,

18. Ga waɗanda suke riƙe da alkawarinsa da gaskiya,Waɗanda suke biyayya da umarnansa da aminci.

19. Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama,Shi yake sarautar duka.

20. Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku,Ku da kuke biyayya da umarnansa,Kuna kasa kunne ga maganarsa!

21. Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da suke a Sama,Ku yabi Ubangiji, ku bayinsa masu aikata abin da yake so!

22. Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa,A duk inda yake mulki!Ka yabi Ubangiji, ya raina!