Littafi Mai Tsarki

Zab 103:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka yabi Ubangiji, ya raina!Ka yabi sunansa mai tsarki!

2. Ka yabi Ubangiji, ya raina,Kada ka manta da yawan alherinsa.

3. Ya gafarta dukan zunubaina,Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.

4. Ya cece ni daga kabari,Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.