Littafi Mai Tsarki

Zab 102:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!

2. Kada ka ɓoye mini sa'ad da nake shan wahala!Ka ji ni, ka amsa mini da sauri sa'ad da na yi kira!

3. Raina ya ɓace kamar hayaƙi,Jikina yana ƙuna kamar wuta.