Littafi Mai Tsarki

Zab 102:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!

2. Kada ka ɓoye mini sa'ad da nake shan wahala!Ka ji ni, ka amsa mini da sauri sa'ad da na yi kira!

3. Raina ya ɓace kamar hayaƙi,Jikina yana ƙuna kamar wuta.

4. An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa,Ba ni da marmarin cin abinci.

5. Ina nishi da ƙarfi,Ba abin da ya ragu gare ni,In banda ƙashi da fata.

6. Ni kamar tsuntsu nake cikin hamada,Kamar mujiya a kufai.

7. Kwana nake ba barci,Na zama kamar tsuntsun da yake fama da kewaA bisa kan ɗaki.

8. Maƙiyana suna cin mutuncina dukan yini.Waɗanda suke mini ba'a,Suna la'antarwa da sunana.

9. Toka ce abincina,Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,

10. Sabili da fushinka da hasalarka.Ka ɗauke ni, ka jefar da ni.

11. Raina kamar inuwar maraice yake,Kamar busasshiyar ciyawa nake.