Littafi Mai Tsarki

Zab 1:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Albarka ta tabbata ga mutumin daBa ya karɓar shawarar mugaye,Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi,Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.

2. Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah,Yana ta nazarinta dare da rana.

3. Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama,Yakan ba da 'ya'ya a kan kari,Ganyayensa ba sa yin yaushi,Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.

4. Amma mugaye ba haka suke ba,Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.

5. Allah kuwa zai hukunta mugaye,Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.

6. Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai,Amma al'amuran mugaye za su watse.