Littafi Mai Tsarki

Yak 5:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙin ciki iri iri da za su aukar muku.

2. Arzikinku mushe ne! Tufafinku kuma duk cin asu ne!

3. Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan!

4. Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.

5. Kun yi zaman duniya da annashuwa da almubazzaranci, ashe, kiwata kanku kuka yi saboda ranar yanka!