Littafi Mai Tsarki

Yak 3:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya , ta Shaiɗan kuma.

16. A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke.

17. Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.

18. Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.