Littafi Mai Tsarki

Mar 7:30-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

31. Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.

32. Suka kawo masa wani kurma mai i'ina, suka roƙe shi ya ɗora masa hannu.

33. Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsotsinsa a kunnuwansa, ya tofar da yau, ya kuma taɓa harshensa.

34. Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”

35. Sai aka buɗe kunnuwansa, aka saki kwaɗon harshensa, ya kuma yi magana sosai.

36. Yesu ya kwaɓe su kada su faɗa wa kowa, amma ƙara yawan kwaɓonsu ƙara yawan yaɗa labarin.

37. Suka yi mamaki gaba da kima, suka ce, “Kai, ya yi kome da kyau! Har kurma ma ya sa ya ji, bebe kuma ya yi magana.”