Littafi Mai Tsarki

Mar 7:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ya ce musu, “Ashe, ku ma ba ku da fahimta ne? Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum daga waje, ba yadda zai ƙazanta shi,

19. tun da yake ba zuciya tasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci.

20. Ya kuma ce, “Abin da yake fita daga cikin mutum yake ƙazanta shi.

21. Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,

22. da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta.

23. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kuwa ƙazanta mutum.”

24. Daga nan kuma ya tashi ya tafi wajajen Taya da Sidon. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa ya sani ba, amma ba ya ɓoyuwa.

25. Nan da nan sai wata mace, wadda 'ya tata ƙarama take da baƙin aljan ta ji labarinsa, ta zo ta fāɗi a gabansa.