Littafi Mai Tsarki

Mar 6:36-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Sai ka sallame su, su shiga karkara da ƙauyuka na kurkusa, su saya wa kansu abinci.”

37. Amma ya amsa musu ya ce, “Ku ku ba su abinci mana.” Sai suka ce masa, “Wato mu je mu sayo gurasa ta dinari metan, mu ba su su ci?”

38. Ya ce musu, “Gurasa nawa gare ku? Ku je ku dubo.” Da suka binciko suka ce, “Ai, biyar ne, da kifi biyu.”

39. Sa'an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna ƙungiya ƙungiya a ɗanyar ciyawa.

40. Haka suka zauna jeri jeri, waɗansu ɗari ɗari, waɗansu hamsin hamsin.

41. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.

42. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi,

43. har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin gurasar da na kifin.

44. Waɗanda suka ci gurasan nan kuwa maza dubu biyar ne.

45. Nan da nan ya sa almajiransa su shiga jirgi su riga shi hayewa zuwa Betsaida, kafin ya sallami taron.

46. Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse domin ya yi addu'a.

47. Da magariba ta yi, jirgin na tsakiyar teku, Yesu kuwa na nan kan tudu shi kaɗai,

48. da ya ga suna fama da tuƙi, gama iska na gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su,

49. amma da suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka zaci fatalwa ce, suka yi kururuwa,

50. domin duk sun gan shi, sun kuwa firgita. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, ni ne, kada ku ji tsoro.”