Littafi Mai Tsarki

Mar 5:42-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Nan take yarinyar ta tashi ta yi tafiya, domin 'yar shekara goma sha biyu ce. Nan da nan kuwa mamaki ya kama su.

43. Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.