Littafi Mai Tsarki

Mar 15:36-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Sai ɗayansu ya yiwo gudu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.”

37. Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, kana ya cika.

38. Sa'an nan labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa.

39. Sa'ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”

40. Akwai kuma waɗansu mata da suke hange daga nesa, cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu ƙarami da Yusufu, da kuma Salome,

41. su ne waɗanda suka biyo shi, sa'ad da yake ƙasar Galili, suna yi masa hidima, da kuma mata da yawa da suka rako shi Urushalima.

42. La'asar lis, da yake ranar shiri ce, wato gobe Asabar,

43. Yusufu ya zo, mutumin Arimatiya, wani ɗan majalisa mai mutunci, wanda shi ma yake sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

44. Bilatus ya yi mamaki ko ya mutu. Sai ya kira jarumin ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa.

45. Da ya san haka daga bakin jarumin ɗin sai ya bai wa Yusufu jikin.