Littafi Mai Tsarki

Mar 15:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus.

2. Bilatus ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗa.”