Littafi Mai Tsarki

Mar 13:35-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne,

36. kada ya zo kwaram, ya samu kuna barci.

37. Abin kuwa da na gaya muku, ina gaya wa kowa ne, shi ne ku zauna a faɗake.”