Littafi Mai Tsarki

Mar 11:27-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Suka koma Urushalima. Yana zaga cikin Haikalin sai manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka zo wurinsa,

28. suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka iznin yin haka?”

29. Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan.

30. To, baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce? Ku ba ni amsa.”

31. Sai suka yi muhawara da juna, suka ce, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’