Littafi Mai Tsarki

Mar 10:8-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Haka su biyun nan su zama jiki guda.’ Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne.

9. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”

10. A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana.

11. Sai ya ce musu, “Kowa ya saki mata tasa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun.