Littafi Mai Tsarki

Mar 10:28-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai, ga shi, mu mun bar kome, mun bi ka.”

29. Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko 'yan'uwansa mata, ko 'yan'uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko 'ya'yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara,

30. sa'an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da 'yan'uwa mata, da 'yan'uwa maza, da iyaye mata, da 'ya'ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami.

31. Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”

32. Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da suke biye kuma suka tsorata. Ya sāke keɓe sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi.

33. Ya ce, “Ga shi, za mu Urushalima, za a ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga al'ummai.

34. Za su yi masa ba'a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”

35. Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.”

36. Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”