Littafi Mai Tsarki

Mar 10:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ya ku 'ya'yana, da ƙyar ne kamar me a shiga Mulkin Allah!

25. Zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

26. Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce masa, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27. Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.”

28. Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai, ga shi, mu mun bar kome, mun bi ka.”

29. Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko 'yan'uwansa mata, ko 'yan'uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko 'ya'yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara,

30. sa'an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da 'yan'uwa mata, da 'yan'uwa maza, da iyaye mata, da 'ya'ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami.

31. Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”