Littafi Mai Tsarki

Mar 1:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.

7. Ya yi wa'azi ya ce, “Wani na zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in sunkuya in ɓalle ba.

8. Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”

9. Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.

10. Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.

11. Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”

12. Nan da nan sai Ruhu ya iza shi jeji.

13. Yana jeji har kwana arba'in, Shaiɗan na gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala'iku kuma suna yi masa hidima.

14. To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,

15. yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”

16. Yana wucewa ta bakin Tekun Galili, sai ya ga Bitrus da Andarawas ɗan'uwansa, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.

17. Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”