Littafi Mai Tsarki

Mar 1:26-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi.

27. Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!”

28. Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.

29. Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya.

30. Surukar Bitrus kuwa na kwance tana zazzaɓi, nan da nan suka ba shi labarinta.

31. Sai ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.

32. Da magariba, bayan faɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu.

33. Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan.

34. Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri iri, ya kuma fitar wa mutane aljannu da yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.

35. Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can.

36. Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi.

37. Da suka same shi, suka ce masa, “Duk ana nemanka.”

38. Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa'azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito.”

39. Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.

40. Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni.”

41. Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.”

42. Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka.

43. Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan,

44. ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka saboda tsarkakewarka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”