Littafi Mai Tsarki

Mar 1:23-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami'arsu, yana ihu,

24. yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

25. Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! Rabu da shi!”

26. Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi.

27. Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!”

28. Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.

29. Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya.

30. Surukar Bitrus kuwa na kwance tana zazzaɓi, nan da nan suka ba shi labarinta.

31. Sai ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.

32. Da magariba, bayan faɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu.

33. Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan.

34. Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri iri, ya kuma fitar wa mutane aljannu da yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.

35. Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can.

36. Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi.

37. Da suka same shi, suka ce masa, “Duk ana nemanka.”

38. Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa'azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito.”