Littafi Mai Tsarki

Mar 1:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa.

22. Sun yi mamakin koyarwa tasa, domin yana koya musu da hakikan cewa, ba kamar malaman Attaura ba.

23. Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami'arsu, yana ihu,

24. yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

25. Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! Rabu da shi!”

26. Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi.

27. Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!”

28. Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.