Littafi Mai Tsarki

M. Had 9:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ka yi nishaɗi da matar da kake ƙauna, dukan kwanakin ranka na banza waɗanda Allah ya ba ka a wannan duniya, ka more kowace rana, wannan ne kaɗai rabonka na wahalar aikinka a duniya.

10. Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.

11. Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyan nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa'a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.

12. Gama mutum bai san lokacinsa ba, kamar kifayen da akan kama da taru, kamar kuma tsuntsayen da akan kama da tarko, haka nan mugun lokaci yakan auko wa 'yan adam farat ɗaya.

13. A duniyar nan na ga wani babban al'amari game da hikima.