Littafi Mai Tsarki

M. Had 5:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Abin da ƙasa take bukata, shi ne sarkin da yake kulawa da aikin gona.

10. Idan kana ƙaunar kuɗi, daɗi ba zai ishe ka ba, wanda kuma yake ƙaunar dukiya, ba zai ƙoshi da riba ba, wannan kuma aikin banza ne.

11. Gwargwadon dukiyarka gwargwadon mutanen da za ka ciyar, ribarka kaɗai ita ce sanin kana da dukiya.

12. Ma'aikaci, ko yana da isasshen abinci, ko ba shi da isasshe, duk da haka yakan ji daɗin barcinsa da dare. Amma mawadaci yakan kwana bai rintsa ba, saboda yawan tunani.

13. Wani mugun abu da na gani a duniyan nan, shi ne mutane sun ajiye kuɗi domin lokacin da za su bukace su.

14. Amma sukan lalace saboda muguwar ma'amala, har ba abin da ya ragu da za su bar wa 'ya'yansu gado.

15. Mukan bar duniyan nan kamar yadda muka shigo ta, ba mu da kome. Dukan ayyukanmu, ba abin da za mu ɗauka mu tafi da shi.

16. Wannan mugun abu ne, mukan tafi kamar yadda muka zo. Mukan yi aiki, muna ƙoƙari mu kama iska, me muka samu ke nan?

17. Mun yi zamanmu a duhu, da baƙin ciki, da damuwa, da fushi, da cuta.

18. Ga abin da na gani yana da kyau, ya kuma dace, shi ne kurum mutum ya ci, ya sha, ya ji daɗin aikin da ya yi a 'yan kwanakin rai da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum.