Littafi Mai Tsarki

M. Had 4:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan na sāke dubawa a kan rashin adalcin da yake ci gaba a duniyan nan. Waɗanda ake zalunta suna kuka, ba kuwa wanda zai taimake su, domin waɗanda suke zaluntarsu suke da iko.

2. Ina ƙyashin waɗanda suka mutu, gama sun fi waɗanda suke da rai yanzu jin daɗi.

3. Amma wanda ya fi su jin daɗi duka, shi ne wanda bai taɓa rayuwa ba, balle ya ga rashin adalcin da yake ta ci gaba a duniyan nan.