Littafi Mai Tsarki

Luk 2:36-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, 'yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci,

37. da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi.

38. Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.

39. Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.

40. Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.

41. To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa.

42. Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin Idi.

43. Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba.

44. Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani.

45. Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa.

46. Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi.

47. Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa.

48. Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”

49. Sai ya ce musu, “Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha'anin Ubana ba?”

50. Amma ba su fahimci maganar da ya yi musu ba.

51. Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.