Littafi Mai Tsarki

Luk 19:46-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

46. ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, ‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu'a.’ Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”

47. Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi.

48. Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.