Littafi Mai Tsarki

L. Mah 3:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Bayan da ya tafi, fādawan suka zo, suka ga ƙofofin ɗakin suna a kulle, sai suka zaci sarkin ya zaga ne ya yi bawali.

25. Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ba, suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe, sai ga ubangijinsu a ƙasa matacce.

26. Sa'ad da suke ta jira, Ehud ya riga ya tsere, ya wuce sassaƙaƙƙun duwatsu zuwa Seyira.

27. Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama'ar Isra'ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba.

28. Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa.

29. A lokacin ne suka kashe ƙarfafan mutane na Mowabawa mutum wajen dubu goma (10,000), ba wanda ya tsira.

30. A ranar nan Isra'ilawa suka rinjayi Mowabawa. Ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya har shekara tamanin.

31. Bayan Ehud kuma, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya kashe Filistiyawa ɗari shida da tsinken korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra'ilawa.