Littafi Mai Tsarki

L. Mah 3:15-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.

16. Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa.

17. Sa'an nan ya ɗauki kyautan, ya kai wa Eglon Sarkin Mowab. Eglon kuwa mai ƙiba ne.

18. Da Ehud ya gama ba shi kyautan, sai ya sallami mutanen da suka ɗauko kyautan.

19. Amma Ehud ya juya ya koma daga wajen sassaƙaƙƙun duwatsu kusa da Gilgal, ya ce wa Eglon, “Ranka ya daɗe, na kawo maka saƙo na asiri.”Sai sarki ya ce wa fādawansa, “Ku ba mu wuri!” Dukansu kuwa suka fita, suka ba da wuri.

20. Ehud kuwa ya je wurinsa, yana zaune shi kaɗai a jinkakken shirayi mai sanyi.Sai Ehud ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah zuwa gare ka!” Sarki kuwa ya tashi daga inda yake zaune,

21. Ehud ya sa hannun hagunsa, ya zaro takobin da suke wajen cinyarsa ta dama, ya kirɓa masa a ciki.

22. Takobin ya shiga duk da ƙotar, kitse ya rufe ruwan takobin gama bai zare takobin daga cikin sarkin ba. Ƙazanta kuwa ta fita.

23. Ehud kuwa ya fita ta shirayin, ya kukkulle ƙofofin ɗakin.