Littafi Mai Tsarki

L. Mah 21:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai mutanen Isra'ila suka zo Betel, suka zauna a nan a gaban Allah har maraice. Suka yi makoki mai zafi.

3. Suka ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa wannan abu ya faru a cikin Isra'ila, har da za a rasa kabila guda ta Isra'ila?”

4. Kashegari mutanen suka tashi da safe, suka gina bagade a can. Suka miƙa hadayun ƙonawa da na salama.

5. Suka kuma ce, “Daga cikin kabilar Isra'ila, wace ce ba ta halarci wannan taro na gaban Ubangiji ba?” Gama sun riga sun yi ƙaƙƙarfan alkawari cewa, “Duk wanda bai hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba, za a kashe shi.”

6. Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi juyayin 'yan'uwansu, mutanen Biliyaminu, suka ce, “Yau an hallaka kabila guda daga cikin Isra'ila.

7. Ƙaƙa za mu yi don mutanen da suka ragu su sami mata. Ga shi, mum riga mu rantse da Ubangiji ba za mu ba su 'ya'yanmu mata su aura ba?”

8. Sa'an nan suka ce, “Wace kabila ce daga cikin kabilar Isra'ila ba ta hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba?.. Sai suka ga, ashe, ba wani daga Yabesh-gileyad da ya halarci taron.