Littafi Mai Tsarki

L. Mah 2:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mala'ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra'ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, ‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba.

2. Ku kuma ba za ku yi alkawari da mazaunan ƙasar nan ba, amma za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya da maganata ba. Me ke nan kuka yi?

3. Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”

4. Da mala'ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi.

5. Saboda haka suka sa wa wuri suna Bokim, wato waɗanda suke kuka. Suka kuma miƙa sadakoki ga Ubangiji a wurin.

6. Da Joshuwa ya sallami Isra'ilawa, kowane mutum ya tafi domin ya ɗauki gādonsa, don ya mallaki tasa ƙasa.

7. Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra'ilawa.

8. Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma.

9. Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash, a ƙasar gādonsa.

10. Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.

11. Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al.