Littafi Mai Tsarki

L. Mah 19:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Baran kuwa ya ce wa maigidansa, “In ka yarda mu ratse mu kwana a birnin Yebusiyawan nan.”

12. Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra'ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya,

13. mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.”

14. Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa'ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu.

15. Suka ratse don su kwana a Gibeya. Balawen ya tafi ya zauna a dandalin garin, gama ba wanda ya kai su gidansa su kwana.

16. To, ga wani tsoho yana komowa daga gona da yamma. Tsohon kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya, amma mutanen Gibeya kabilar Biliyaminu ne.

17. Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”

18. Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungun da take ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa.

19. Ina da baro domin jakuna, ina kuma da abinci da ruwa inabi don kaina, da ƙwarƙwarata da barana, ba mu rasa kome ba.”

20. Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.”