Littafi Mai Tsarki

L. Mah 16:24-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Da mutane suka gan shi, sai suka raira waƙar yabon allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya ba da maƙiyinmu a hannunmu, wanda ya fallasa ƙasarmu, ya kashe mutanenmu da yawa.”

25. Sa'ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.

26. Samson kuwa ya ce wa yaron da yake jagoransa, “Bari in taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da gidan nan, domin in jingina.”

27. Gidan kuwa yana cike da mutane mata da maza. Shugabannin nan biyar na Filistiyawa suna wurin. Akwai mutum dubu uku mata da maza, a kan benen da suka zo kallon wasan Samson.

28. Sa'an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.”

29. Sai Samson ya kama ginshiƙai biyu da suke a tsakiya, waɗanda suke ɗauke da gidan. Ya riƙe su da hannunsa biyu, ɗaya a kowane hannu, sa'an nan ya jingina jikinsa a kansu,