Littafi Mai Tsarki

L. Mah 11:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa.

2. Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.”