Littafi Mai Tsarki

L. Fir 8:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa,

2. “Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti.

3. Ka kuma tattara jama'a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”

4. Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama'ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada.

5. Musa ya faɗa wa taron jama'ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”

6. Sai Musa ya fito da Haruna da 'ya'yansa maza, ya yi musu wanka.

7. Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.

8. Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen.